Al’ummar ƙauyen Damari da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna suna ƙoƙarin tantance ɓarnar da ƴan bindiga suka tafka a wani hari da suka kai jiya Alhamis da daddare.
Barnar ta yi sanadiyyar kashe mutum biyar da kuma sace wasu, waɗanda har yanzu ba a tantance yawansu ba.
Shugaban ƙungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari, Ishak Usman Kasai ya tabbatar wa BBC cewar, ɓarayin sun shiga ƙauyen ne a wani lamari mai kama da ramuwar gayya bayan artabun da suka yi a ranar Litinin da wasu, waɗanda ake zargin mayaƙan ƙungiyar Ansaru ne, waɗanda ke gudanar da lamurransu a yankin.