fidelitybank

Muna takaicin hare-haren da ake kai wa ofisoshin mu – INEC

Date:

Wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke karamar hukumar Orlu a jihar Imo.

Masu kone-kone sun kai hari a ginin da ake yi wa kwaskwarima a ranar Alhamis.

Kwamishiniyar zabe ta INEC reshen jihar Imo, Farfesa Sylvia Agu, ta tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da kwamishiniyar yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ta fitar a jiya, kamar yadda NAN ta ruwaito.

“Al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis, 1 ga Disamba, 2022.

“Gini, wanda ake yin gyare-gyare sosai bayan harin da aka kai a baya, an lalata shi kuma an kone shi a wani bangare,” in ji shi.

Okoye ya ce, an yi garkuwa da wasu daga cikin wadanda ke aiki a wurin amma daga baya aka sake su.

Ya bayyana cewa, shiga tsakani da ‘yan sandan da aka tura wurin suka yi a kan lokaci ya rage barnar da aka samu.

“Da ma barnar ta fi yawa amma ga gaggawar da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayar wanda ta tura jami’anta zuwa wurin.

“Wannan hari daya ne ya yi yawa,” in ji shi.

INEC ta nuna damuwarta kan hare-haren da aka kai kan cibiyoyinta a fadin kasar nan gabanin babban zabe na 2023.

Hukumar ta lura cewa irin wadannan hare-haren suna da mummunan sakamako kan shirye-shiryenta na 2023.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp