An gano cewa daruruwa a Burtaniya sun kulla auratayya da ‘yan kasar don kawai su mallaki fasfonta, kuma hukumomi na sane amma ba su ce uffan ba.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta gano cewa an kulla irin wadannan auratayya kusan 400 daga 2018 zuwa yanzu.
BBC ta fahimci cewa mutum tara kawai aka taba kamawa da laifin aikata hakan.
Sai dai a yanzu ma’aikatar harkokin cikin gidan ta ce ba za ta yi kasa a gwuiwa ba, wurin ganin ta dauki matakin da ya dace ga duk wanda ke da hannu ga hada irin wannan auratayya.