Jami’an ‘yan sanda a jihar Kano, sun ayyana neman wasu mutum saba’in da biyu ruwa a jallo, bisa zargin aikata laifin fashi da makami da aikata daba.
Mutanen suna cikin tubabbun ‘yan daba 623 da suka mika wuya ga ‘yan sanda a kwanakin baya, karkashin shirin zaman lafiya da yi musu afuwa.
‘Yan sanda sun ce sun gano wani da ya mika kansa a baya, a yanzu yana jagorantar gungun wasu matasa suna tayar da hankalin mutane a unguwanni da dama ciki har da yankin Dala.
Kwamishinan ƴan sanda a jihar ta Kano, CP Muhammad Hussaini Gumel ya ce wadanda ba su fandare ba za su taimaka musu su zama masu amfani a cikin al’umma:


