Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta bukaci tallafin sojoji domin dakile duk wani abu da ya shafi tsaro a rumbunan abincin ta dake Kaduna.
Kodinetan NEMA na shiyyar arewa maso yamma, Imam Garki ne ya yi wannan kira a lokacin da ya ziyarci kwamandan runduna ta biyu ta sojojin Najeriya, ranar Talata a Kaduna.
Ya ce sun kai ziyarar ne domin karfafa tsaro a rumfunan ajiya daban-daban, biyo bayan aukuwar lamarin da wasu ‘yan daba suka kai hari a cibiyoyin gwamnati domin kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.
“Muna nan ne don neman tallafin sojoji don samun matsayin jami’an tsaro na jiran aiki don kiyaye wuraren ajiyar kayayyakin hukumar,” in ji shi.
Ko’odinetan wanda ya samu wakilcin shugaban sashen bincike da ceto na hukumar Abdulkadir Mohammed ya jaddada cewa hukumar na da alaka da rundunar sojojin Najeriya, wanda ke aiki a matsayin daya daga cikin sassan da ke ba da agajin gaggawa (DRUs) na hukumar. .
Da yake mayar da martani, Lt.-Col. Abdulqadir Abdullahi, Kwamandan Bataliya ta 2 na Sojojin Najeriya, ya tabbatar wa hukumar hadin gwiwa da rundunar ta Sojoji wajen shawo kan lamarin.
Babban Darakta, Mista Mustapha Ahmed, ya umurci Daraktocin shiyya da shugabannin ayyuka da su karfafa tsaro a ofisoshin NEMA da ma’aikatun NEMA da kewaye a fadin kasar nan.