Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ta yi kira ga mutumin a wani faifan bidiyo da ya yi zargin cewa wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai masa hari a Lekki jihar Legas domin ya fito ya taimaka wajen gudanar da bincike kan lamarin.
Bidiyon wani matashi da ya yi zargin cewa ‘yan ta’adda ne suka dauke shi a zagayen Ikoyi da ke Lekki a cikin kayan sojoji ya bazu a shafukan sada zumunta.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa wannan ikirari karya ce, inda ya bukaci wanda ake zargin ya bayyana a ofishin.
A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, PPRO ya ce rundunar ba za ta bar wani abu ba tare da tabbatar da tsaron mazauna Legas da masu ziyara.