Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta tsawaita rajistar masu kada kuri’a a kasar nan.
A cewar jam’iyyar, akwai kuma bukatar a samar da karin cibiyoyin rajista a yankin Arewa maso Yamma.
Ta bayyana cewa, har yanzu akwai mutane da dama da ba a yi musu rijista ba, saboda karancin cibiyoyi, don haka ake bukatar tsawaita aikin.
“A matsayinmu na jam’iyyar siyasa, muna kira ga INEC da ta duba ciki ta kuma tsawaita aikin rajistar don baiwa mutane da dama damar yin rajista. Muna kuma son su samar da karin wuraren yin rajista” .