Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso ya kawo karshen rade-radin da ake yi na cewa zai marawa wata jam’iyya.
Da yake magana ta bakin mai magana da yawunsa, Ladipo Johnson, Kwankwaso ya ce, babu maganar janyewa yakin neman zabensa ga wani.
Ladipo ya yi wannan tsokaci ne a gidan talabijin na Channels Television Sunrise Daily a ranar Laraba a yayin da ake ta rade-radin cewa jam’iyyar NNPP za ta ruguza yakin neman zabenta na neman wani dan takarar shugaban kasa kafin 2023.
“Abin da nake nufi lokacin da na ce ba tukuna ba shine cewa za mu tafi har zuwa 25 ga Fabrairu na shekara mai zuwa,” in ji shi.