Sanata Ben Obi da Farfesa Obiora Okonkwo, shugaban da Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Atiku da Okowa a jihar Anambra, sun bayyana cewa wata tawaga ta musamman na kokarin sasanta rikicin da ke tsakanin dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar da gwamnonin G5.
Sun bayyana hakan ne a ranar Laraba a garin Awka na jihar Anambra, yayin wani taron manema labarai na tunkarar yakin neman zabe domin sanar da ziyarar Alhaji Atiku Abubakar a ranar Alhamis.
Majalisar kamfen din ta kuma yi amfani da damar wajen gabatar da shirinta na tunkarar dan takarar a jihar Anambra.
Sanata Ben Obi da Okonkwo da suka yi wa manema labarai jawabi sun ce ana ci gaba da kokarin sasanta Atiku da Gwamnonin G5, kuma jihar ta shirya tsaf don baiwa Atiku nasara a zaben 2023.
Obi ya ce: âAbu ne na kowa ga jamâiyyun siyasa su yi rikici. Hakan bai wuce inda ake ba, kuma muna da wata tawaga da ke kokarin ganin an warware rikicin da ke faruwa a PDP.
âWannan ba abu ne da muke son bayyanawa jamaâa ba, amma bari in gaya muku cewa gwamnonin G5 ma suna son a samu zaman lafiya, Wike (Gwamnan Jihar Ribas) ya fadi haka. Muna da tawaga da ke aiki a kan hakan, kuma a yanzu, ba mu son bayyana sakamakon ga jama’a, amma muna aiki.”
Okonkwo ya kuma kara da cewa: âKo a jihohin da ake fama da wannan rikici, har yanzu ana ci gaba da yakin neman zabe, kuma shirin shi ne zaben PDP daga sama har kasa. A Abia kun ji taken sama da biyar, kuma duk gwamnoninmu suna ta yakin neman zaben Atiku.
âA dukkan bukatun su (G5) ba su taba cewa suna da wata matsala da Atiku da kan su ba. Ba alâamari ne da ba za a iya warware shi ba.â
Da yake magana a kan shirin dan takarar a Anambra a ranar Alhamis, Okonkwo ya ce jamâiyyar na sa ran za a gudanar da gagarumin gangami, kuma an shirya masa ayyuka da dama.
âZuwa da karfe 10 na safe, za mu hadu da shi a filin jirgin sama sannan mu wuce zuwa masaukin Gwamna, inda dan takarar shugaban kasa zai gana da Gwamna Chukwuma Soludo. Daga nan ne zai yi wata ganawa ta bangaranci da sarakunan gargajiya na jihar Anambra.
“Zai kaddamar da ofishin yakin neman zabe, sannan kuma zai yi mu’amala da shugabannin kungiyar, shugabannin kasuwa, a cibiyar Ekwunife, kafin kaddamar da yakin neman zabe.”
A baya dai jamâiyyar ta bada sanarwar hutu a tsakanin daukacin âyaâyan jamâiyyar PDP na jihar, kuma Okonkwo ya ce matakin ya tsaya, kuma ana sa ran samun dimbin jamaâa a yakin neman zaben.