Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammed Bin Salman, ya yi kira ga ƙasar Iran da ta hada kai da ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen yankin Larabawa, tare da daina tsoma baki a al’amuran da suka shafi harkokin cikin gida na ƙasashen.
Yariman ya yi wannan kira ranar Asabar yayin bikin bude taron ƙoli na ƙungiyar da ke gudana a birnin Jidda na kasar Saudiyya. Kamar yadda jaridar Saudi gazzet ta ruwaito.
Ƙasashe mambobin ƙungiyar shida tare da ƙasashen Masar, da Jordan da kuma Iran ne ke halartar taron.
A jawabin buɗe taro Yariman na Saudiyya ya ce ana buƙatar haɗin kai domin taimakawa wajen farfaɗo da tattalin arziki duniya, sannan kuma ya yi gargaɗin cewa rashin tsari mai kyau game da makamashi ka iya haifar da hauhawar farashi a kasuwannin duniya.