Shugaban Guinea- Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce har yanzu Ecowas na kan matsayinta na amfani da ƙarfin soji a Nijar.
Cikin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labaran France24, Embalo ya koka kan yawaitar juyin mulki a yankin yammacin Afirka cikin shekarun baya-bayan nan, sannan ya yi magana kan rawan da Ecowas ke taka wa wajen hana aukuwar hakan.
Mista Embalo ya bayyana juyin mulkin da ake a yankin yammacin Afirka da cewa yi wa dimokraɗiyyar yankin tarnaƙi ne.
Yana mai cewa rashin ɗaukar matakai kan juyin mulkin da ake yawan yi a yankin, ka iya rage kimar Ecowas.
“Ecowas ta ɗauki matakin girke sojojinta, kuma mun gudanar da taruka har guda biyu game da haka a Najeriya”, in ji shi.
Tun da farko ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar amfani da ƙarfi soji don mayar da hamɓararren shugabna Nijar Mohamed Bazoum, idan duka hanyoyin tattaunawar diplomasiiya suka ci-tura.


