Kakakin kungiyar yakin neman zaben Tinubu/Shettima, Festus Keyamo, ya jajanta wa mawaki David Adeleke da amaryarsa Chioma Rowland bisa rasuwar dansu, Ifeanyi.
Rahotanni sun ce Ifeanyi ya nutse a ranar Litinin a gidan mawakin na Banana Island.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, ta kuma ce an kawo ma’aikatan gida takwas domin yi musu tambayoyi kan lamarin.
Da yake mayar da martani, Keyamo ya jajantawa iyalan.
Ya rubuta, “A gaskiya ina jiran bayanin iyali kan wannan don in tabbata. Ta’aziyyata ga wannan matashin iyali da suka fuskanci wannan bakin ciki a wannan lokaci.
“Allah Madaukakin Sarki Ya ba iyalan Adeleke kwarin guiwar jure wannan rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba; da kuma duk wadanda suka sha irin wannan rabo”.
Shima da yake mayar da martani, mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed ya yi addu’ar Allah ya jikan ma’auratan.
“Tunanina da addu’a na tare da @Davido, wanda ya yi rashin dansa, Ifeanyi. Babu wani iyaye da ya isa ya fuskanci rasa ɗa a cikin irin wannan mummunan lamari.
“Allah ya jikan shi da Chioma, uwar yaron.”