Wata kungiyar Arewa a karkashin kungiyar Arewa Development Forum for Peace and Justice (ADFPJ) ta goyi bayan kiran da gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle ya yi na cewa, jama’a su mallaki bindigogi, domin kare kansu daga ‘yan fashi da ke addabar al’ummarsu.
Kungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata ta hannun Shugaban Hukumar, Alhaji Zubairu Mustafa, ta kuma yi kira ga gwamnonin Arewa da su bi matakan da Matawalle suka dauka na kafa ‘yan sa-kai na ‘yan banga na al’umma, domin kara kaimi ga kokarin hukumomin tsaro a yankin.
Da take yabawa musamman ga kungiyar kare hakkin jama’a (CPG) da Matawalle ta kaddamar a Zamfara ranar Asabar, kungiyar ta ce, sukar da suka biyo bayan matakan tsaro ba su da tushe balle makama daga wadanda ba sa fatan zaman lafiya ya dawo jihar da kuma Arewa baki daya.