Kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC a ranar Asabar din da ta gabata ta bukaci gwamnatin tarayya da ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin kare lafiyar ‘yan kasar sakamakon yakin da ake yi a kasar Sudan.
Mista Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC ne ya bayyana hakan a Abuja cikin wata sanarwa mai taken, “Kada ‘yan Najeriya a Sudan su mutu”.
Sanarwar ta kara da cewa, “Mun sanya ido sosai tare da yanke kauna ga bala’in da ke faruwa a Sudan sakamakon yakin da ake yi a kasar.
“Bai kamata a bar ‘yan Najeriya su mutu a Sudan ba saboda sakaci. Bai kamata a yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu da kuma kwashe su zuwa Najeriya idan yakin ya ci gaba da rikidewa zuwa yakin basasa.
“Har yanzu aikin gwamnati ne kuma muna kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da hakan.”
A halin da ake ciki, Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Honarabul Abike Dabiri-Erewa, ta ce kwanan nan kona jiragen sama a filin jirgin saman kasar na iya kawo cikas ga kwashe ‘yan Najeriya da ke makale a Sudan.


