Ƙungiyar da ke sa ido kan harkokin zaɓe a Najeriya wato TMG, ta gargaɗi masu riƙe da muƙaman gwamnati a kan amfani da dukiyar ƙasa wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe da sauran harkokin jam’iyya.
Ƙungiyar ta ce, ta lura da yadda wasu manyan jami’ai, ciki har da ministoci, suke amfani da kayan gwamnati kamar jiragen sama da motoci, har ma da kuɗaɗe wajen yin kamfen.
Shugaban ƙungiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya shaida wa BBC cewa abu ne da ba za a lamunta da shi ba, kuma ya yi ikirarin cewa a gwamnantin Muhammadu Buhari ce kadai aka samu irin wannan karya doka.
Ya kuma nuna damuwa a kan makudan kudaden da masu rike da mukaman gwamnati suka kashe wajen sayan fom din tsayawa takara.