Kungiyar Gwamnoni ta NGF, ta ba da tabbacin cewa tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago za su haifar da ingantaccen albashi.
Da yake tashi daga taron da ta yi da sanyin safiyar ranar Alhamis, NGF a cikin wata sanarwa da shugabanta kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRazaq AbdulRahman ya fitar, ya ce sun amince da ci gaba da yin cudanya da masu ruwa da tsaki domin cimma matsaya mai kyau.
Batun mafi karancin albashi na kasa ya ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce musamman bayan da Gwamnonin suka yi tazarce a kan Naira 62,000 da Gwamnatin Tarayya da masu zaman kansu suka bayar a kwamitin uku.
“Zauren ya samu bayani daga Ministar Harkokin Mata kan Bankin Duniya-Najeriya kan Matakan Ayyukan Mata, tare da sauran ayyukan ma’aikatar. Mambobin sun bayyana mahimmancin aikin tare da jaddada bukatar aiwatar da shi a matakin jiha kamar yadda aka tsara tun farko, kasancewar jihohi ne farkon fara aikin.
“Gwamnonin sun amince da aiki da gudummawar da ma’aikatar harkokin mata ke bayarwa wajen inganta daidaiton jinsi, karfafa mata, da kuma ci gaban zamantakewa a fadin Najeriya.
“Majalisar ta tattauna kan sabon mafi karancin albashi na kasa. Gwamnonin sun amince da ci gaba da yin cudanya da manyan masu ruwa da tsaki domin cimma matsaya mai dacewa. Mun ci gaba da sadaukar da kai ga tsarin kuma muna ba da tabbacin cewa za a samu mafi kyawun albashi daga tattaunawar da ake yi,” in ji sanarwar.
Gwamnonin sun kuma tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi kasar nan, da suka hada da manufofin kasafin kudi da garambawul.