Ƙungiyar manoma ta ƙasa a Najeriya, AFAAN, ta bayyana jin daɗi da goyon bayanta kan matakin gwamnatin tarayya na raba wa gwamnatocin jihohi buhunan kayan abinci da na noma.
A watan da ya gabata ne Shugaba Bola Tinubu, ya ba da umarnin a raba wa jihohin buhunan shinkafa da masara 100,000, da takin zamani 100,000 a matsayin tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin mai.
Sai dai mai magana da yawun kungiyar manoman ta Najeriya, Muhammad Magaji, ya ce, suna fargabar hakan ka iya haifar da ƙaranci da tsadar abinci a kasuwa.
A cewarsa, a yanzu babu wadataccen abincin a hannun manoma. “Idan gwamnati ta saye wanda ya rage a kasuwa hakan zai kawo ƙarancin abincin wanda zai sa ya yi tsada.” A zantawa da BBC.