fidelitybank

Muna da isassun bayanai dake nuna jami’an gwamnati na tattaunawa da ‘yan bindiga – Zamfara

Date:

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa gwamnatinsa na da isassun bayanai da ke tabbatar da cewa akwai wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da ke jagorantar tattaunawar sirri da ƴan fashin daji a jihar.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a wani martani da ya mayar wa Gwamnatin Tarayya, a yau Talata, bayan wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar Litinin tana ƙalubalantar gwamnan game da zargin da ya yi na cewa Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da ƴan bindiga a jihar.

Sanarwar da ta fito daga ministan yaɗa labaru da wayar da kan al’umma na Najeriya, ta zargi gwamnan na Zamfara da sanya siyasa cikin harkar tsaro.

Sai dai a martanin da ya mayar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Bala Idris, gwamnan na Zamfara ya ce “muna da sahihan bayanai da shaidu game da abin da ya faru tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da ƴan fashin daji a lokacin jerin tattaunawar da aka yi a wurare daban-daban a jihar Zamfara.”

Amma sanarwar ta ce gwamnatin Zamfara ba ta da niyyar fallasa sunayen wakilan Gwamnatin Tarayyar da suka yi tattaunawar a kafafen yaɗa labaru saboda girmama hukuma da kuma tsarin doka.

Haka nan gwamnatin jihar ta soki lamirin ministan yaɗa labarun na Najeriya kan martanin da ya mayar mata a ranar Litinin, inda ta ce ya yi hakan ne ba tare da yin binciken da ya dace ba.

Ita dai gwamnatin Zamfara ta ce an gudanar da tattaunawar da ta yi magana a kai ne a yankunan Birnin Magji da Maradun da Mun Haye da Ajah da Bawo da kuma Bagege.

A martanin na ranar Talata, gwamnatin Zamfara ta ce “Tattaunawa da ƴan bindiga babban kuskure ne wanda ba za ta so ta aikata ba, kuma hakan ba zai kawo ƙarshen matsalar ba, face ma, ya ƙara ƙarfafa wa ƴan fashin gwiwa.”

A ranar Litinin ne dai Gwamnatin Tarayya a cikin sanarwar da ta fitar ta ce “Babu wani jami’in gwamnatin Tarayya da ke tattaunawa da wani ɗan bindiga ko ƙungiyar ƴan bindiga.”

“Sai dai gwamnatin a shirye take ta yi amfani da duk wata hanya wajen sassauta yanayi na tashin hankali da ake ciki da kuma mayar da zaman lafiya a yankunan da ƴan fashin daji suka addaba.”

Zamfara dai na a sahun gaba cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da matsalar rashin tsaro ta ƴan fashin daji ke ci gaba da yi wa illa.

Ko a makon da ya gabata, ƴan daji sun kai hari a gidajen kwanan ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, inda suka yi awon-gaba da ɗalibai da dama, waɗanda har yanzu wasu daga cikin su ke hannun ƴan fashin.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp