Hukumar da ke yaki da cutuka masu saurin yaduwa ta NCDC, ta ce, tana cikin shirin ko-ta-kwana, bayan da aka samu bullar cutar Marburg a kasar Ghana.
A wata sanarwa da hukumar ta NCDC ta fitar ta ce Najeriya ta tanadi abubuwan gwaje-gwajen gano cutar da kuma yadda za su magance ta idan ta bulla a kasar..
Ta kara da cewa likitocin kasar sun shirya wa cutar ta Marburg mai alaka da Ebola, an kuma tsaurara matakan sa-ido kan cutar.
Kawo yanzu dai ba a samu rahoton bullar cutar a kasar ba, wacce ta fi kowacce kasa yawan al’umma a nahiyar Afirka.
A farkon makon nan ne dai,hukumomin lafiya a Ghana suka tabbatar da bullar cutar a kasar, inda mutum biyu da aka tabbatar na dauke da cutar suka mutu, yayin da aka killace gomman mutane.