Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas, ta yi kira ga Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike da ya dawo jam’iyyar saboda ana bukatarsa.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Tony Okocha, ya ce jam’iyyar ce ke kan mulki, don haka ya kamata Wike ya shiga.
Ya zanta da manema labarai a Fatakwal bayan ‘yan majalisar jihar 27 sun koma APC.
Da aka tambaye shi ko sauya shekar wani bangare ne na shirin Wike ya koma APC, Okocha ya ce: “Bana tunanin haka.
“Ko menene dalilinsu idan sun isa gadar za su tsallaka ta.
‘’Wike dan siyasa ne da sunansa ya girgiza a cikin al’umma; don haka babu wanda zai iya tunani ko ya ce masa idan zai koma APC ko a’a.
“A 2023, ya taimaka kwarai da gaske wajen nasarar APC a jihar.
“Mafi kyawun abin da muke rokonsa ya yi shi ne ya zo ya koma jam’iyyar APC domin ita ce ke mulki.”