Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce tana duba bidiyon da aka nada a filin wasan Old Trafford wanda ya nuna yadda wasu magoya bayan kungiyar suka rika jifa da wasu abubuwa yayin da kungiyar ta sha kaye a hannun Atletico Madrid ta ci daya mai ban haushi.
Wasunsu sun jefi kocin kungiyar ta Atletico Madrid, Diego Simeone da abubuan da suka hada da kwalabe bayan da aka kammala wasan.
Hukumar da ke shirya gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA na jiran rahoton da ‘yan kallon da ta tura za su mika ma ta kafin ta dauki mataki.
Duk wanda aka samu da laifin yin jifa a filin wasan kwallo ya taka dokar wasa kuma ana iya hana shi halartar wasanni a filayen wasa na tsawon shekara uku.