fidelitybank

Muna bincike akan Budurwar da ake zargi ta rataye kanta a Kano – Ƴan Sanda

Date:

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce,  tana ci gaba da bincike kan abin da ya sa wata budurwa mai shekara 17 ta rataye kanta a ƙauyen Garin Dau da ke yankin karmar hukumar Warawa.

Mafi akasarin mazauna ƙauyen dai sun yi zargin cewar, budurwar ta rataye kan nata ne, bisa auren dole da iyayenta ke shirin yi mata.

Sai dai iyayen nata sun musanta wannan zargi, inda suka ce, ba ta kammala makarantar sakandare ba, balle a yi maganar aurar da ita.

Faruwar wannan lamari dai ya ya zowa mazauna yankin da mamakin, sakamakon yadda da dama daga cikin mutanen kauyen ke bayyana budurwar da kyawawan ɗabi’u.

A yau ne aka shiga yini na biyu na rasuwar Safiya mai shekaru 17 da ke aji biyu a makarantar sakandare, wadda aka tarar da gawarta a rataye kuma ana zargin ita ta rataye kanta.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne mai magana da yawun rudunar ƴan sanda a Kano, ya shaida wa BBC cewa, sun sami labarin faruwar lamarin, kuma suna bincike kan lamarin, domin gano shin budurwar ce ta rataye kan nata ko kuwa.

Wannan dai shi ne rahoton rataye kai na baya-bayan nan da aka samu a Kano, sabanin a watanin baya da suka gabata, biyo bayan kiraye-kiraye da wayar da kan al’umma da hukumomin suka dauka.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp