Dan takarar gwamna na jam’iyyar Action Alliance (AA) a zaben 2023 a jihar Kaduna, Timothy Adamu, ya bayyana kaduwarsa da kisan gillar da wasu ‘yan bindiga suka yi wa Misis Victoria Chimtex.
A wata sanarwa da shi da kansa ya fitar a Kaduna ranar Larabar da ta gabata, ya ce, ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka harbe Misis Victoria Chimtex a gidanta da misalin karfe 8:30 na daren ranar Litinin, kuma mijin da kyar ya tsallake rijiya da baya sakamakon raunukan da maharan suka yi masa a kafarsa. Wannan lamari ne mai matukar tayar da hankali cewa za a iya kai wa irin wannan iyali hari a yankunan karkara.”
Ya kara da cewa, “Misis Victoria Chimtex ta kasance mamba ce mai karfi a jam’iyyar Labour wadda shahararta ta shahara a tsakanin al’umma. Ya kamata mu koyi yin siyasa ba tare da wani abu na dacin rai ba, kuma a yi hakan domin ci gaban al’umma baki daya”.
Ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ‘yan uwa, yana mai cewa abin damuwa ne kuma ya kamata ‘yan Najeriya su yi Allah wadai da shi, domin ya kamata a rika kallon siyasa a matsayin bayyana manufofin yadda ake tafiyar da al’umma.