Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa domin bunƙasa harkar noma da kuma samar da abinci a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da shugaban Brazil Inacio Lula Da Silva, a daidai lokacin da ake fara taron ƙungiyar ƙasashe ta Brics karo na 17.
A cewar sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce wasu tsare-tsare mara kyau a baya sun taimaka wajen hana samun cigaba a ɓangaren noma a ƙasar.
Shugaban ya fada wa takwaransa na Brazil cewa tuni Najeriya ta fara aiwatar da wasu manufofi domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar wanda zai yi gogayya da sauran duniya, musamman a ɓangaren noma.
Ya ƙara da cewa a shirye Najeriya take wajen kulla hulɗa da Brazil don ganin an ɗauki mataki nan take wajen ƙara bunƙasa samar da abinci.
“Za mu aiwatar da duk yarjejeniya da muka amince da Brazil, domin kawo gyara a ɓangaren kasuwanci, sufurin jiragen sama, makamashi, samar da abinci da kuma haƙar ma’adinai,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce gwamnatinsa na ƙoƙari don bunƙasa harkar kiwon dabbobi.
A nasa ɓangare, shugaba Lula ya tabbatar da cewa za a aiwatar da duk wata yarjejeniya da aka cimma da Najeriya ba tare da ɓata lokaci ba, don ganin kyautatuwar tattalin arziki da kuma hulɗa tsakanin ƙasashen biyu.