Mukaddashin shugaban jami’ar tarayya ta Gusau, Farfesa Aliyu Gadanga Tsafe, ya ce mahukuntan cibiyar da jami’an tsaro suna aiki kafada da kafada da su wajen ganin an ‘yantar da wasu daliban da aka sace kwanan nan a unguwar Damba da ke Gusau.
Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa, Tsafe ya bayyana cewa ba a sace daliban a harabar jami’ar ba.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da masu zuba jari da masu hannu da shuni da su kawo agajin cibiyar ta hanyar samar da masauki ga dimbin daliban jami’ar saboda ayyukan ‘yan fashi da suka addabi cibiyar.
Tsafe ya dora laifin sace-sacen da ake yi a makarantar a kan rashin isassun katanga da kuma dakunan kwanan dalibai, inda ya ce mahukuntan makarantar ba su ji dadin yadda daliban ke zama a wajen harabar makarantar ba.
Mukaddashin shugaban jami’ar ya ce ana bukatar karin kudade domin kafa shingen kariya ga daliban da ma’aikatan makarantar.
“Ba mu da isasshen wurin kwana ga dalibai da ma’aikata a makarantar,” in ji shi.
Ku tuna cewa an yi garkuwa da wasu daliban Jami’ar a ranar Juma’ar da ta gabata.


