Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ce, gwamnatinsa tana aiki tuƙuru domin sake gyara tattalin arzikin ƙasar ta yadda za a mayar da hankali kan samar da manyan ayyuka tare da sabunta ayyukan more rayuwa.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka jiya Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC a jihar Legas.
A cewarsa, “ina sa ran za a fitarda kasafin kuɗi kowane lokaci daga yanzu, za ku ga yadda aka karkata kan manyan ayyuka, dole ne sabunta lalacewar ayyukan more rayuwa, mu kuma gyara hakan tare.”
Ya kuma bayyana damuwa game da yawan yaran da basa zuwa makaranta a ƙasar bayan rahoton baya-bayan nan da aka fitar.
“Ya zama dole mu magance wannan matsala ta hanyar samar da ƙarin makarantu da ɗiban malamai aiki da samar da tsarin ciyar da ɗalibai.” kamar yadda Tinubu ya bayyana.
Shugaba Tinubu ya ce dole ne dimokraɗiyya ta ci gaba kuma ta tafi da kowa da zummar magance talauci ta hanyar samar da damarmaki na aiki ga matasa da kuma inganta ilimin yaran Najeriya.
Ya ce yin haɗin gwiwa da ɓangarorin gwamnati da dama abu ne mai muhimmanci wajen ci gaban gwamnatinsu da kuma Najeriya.
A nasa ɓangaren, shugaban Jam’iyyar APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da Tinubu cewa kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya yi tsare-tsaren tabbatar da nasarar APC a zaɓen cike gurbin da ke tafe a watan Fabarairun 2024.


