fidelitybank

Muna ƙoƙarin kuɓutar da Sarkin Gurku da iyalinsa – ‘Yan Sanda

Date:

Rundunar ƴan sanda a jihar Nasarawar ta ce, jami’anta na can suna ƙoƙarin kuɓutar da mai martaba Sarkin Gurku da iyalinsa, waɗanda ƴan bindiga suka sace.

Rundunar `yan sandan ta tabbatar da cewa da misalin karfe goma na dare, maharan waɗanda ake zargin masu satar mutane ne ɗauke da bindigogi suka kutsa fadar mai martaba Sarkin Gurku, mai daraja ta ɗaya, Alhaji Jibrin Mohammed, bayan sun kaikaici lokacin da aka watse daga fada, wadda ke da tazarar kilomita goma da marabar Gurku da ke jikin babbar hanyar da ta tashi daga Abuja ta dangana da Keffi, inda suka tafi da shi da mai ɗakinsa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar ta Nasarawa, Rahman Nansel, ya ce an yi wa rundunar `yan sanda kiran neman ɗauki a ranar 6 ga watan Agusta, cewa wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun kai samame fadar mai martaba sarkin Gurku.

Nan da nan kwamishinan `yan sanda ya tura jami’ansa zuwa fadar tare da haɗin-gwiwa da ƴan banga.

Suna isa suka tarar an sace sarkin da iyalinsa, kuma ba a san inda aka tafi da su ba. An karaɗe dazukan da ke kewaye amma ba a yi nasarar samun su ba.“

Kakakin ƴan sandan ya ce jami`ansu sun bazama, suna ƙoƙarin gano maɓoyar ‘yan bindigan don ceto basaraken da mai ɗakin nasa.

Jihar Nasarawa na maƙwabtaka da jihohi da dama da ke fama da ƙalubalen da ya shafi tsaro, ciki har da Binuwai da Plateau da Kaduna da Kogi da kuma Abuja, babban birnin tarayya.

Ko a watan jiya, gwamnan jihar Abdullahi Sule ya nuna damuwa game da yadda miyagun da aka fatattaka a jihohi makwabta ke kwarara jiharsa. Har ma ya buƙaci hedikwatar tsaron Najeriya da ta taimaka wajen dakile miyagun.

latest news in nigeria today 2022 punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...
X whatsapp