fidelitybank

Muna ƙoƙarin kafa hukumar ƙayyade farashin kayayyaki – Gwamnatin Tarayya

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, tana aiki domin kafa hukumar ƙayyade farashin kayayyaki a matsayin maslaha ga hauhawar farashin kayan masarufi a ƙasar.

Ana sa ran hukumar za ta yi nazari tare da daidaita farashin kayan masarufi da kuma kula da muhimman rumbunan abinci don daidaita farashin hatsi da sauran kayan abinci.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana haka ranar Talata a wani taron yini biyu da aka yi kan sauyin yanayi da tsarin abinci da kuma tattara albarkatun kasa da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sanata Shettima ya ce, taron na nuna ƙoƙarin Najeriya na rage mummunan tasirin sauyin yanayi da tabbatar da samar da abinci.

Mataimakin shugaban ƙasar wanda ya yi bayani kan gyare-gyaren manufofi da gwamnati ta yi domin samar da abinci da ruwan sha, ya ƙara cewa maslaha ga matsalar abinci ya zama abu na gaggawa da matsakaici da dogon zango inda ya bayyana cewa tsarin matsakaicin zango ya ƙunshi farfaɗo da samar da abinci ta hanyar tallafi kamar rarraba taki da hatsi ga manoma da gidaje domin rage raɗadin cire tallafin mai da kuma magance banbancin farashin abinci ta hanyar kafa hukumar da za ta kula da farashin kayayyaki ta ƙasa.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp