Gwamnatin jihar Kogi ta ce, tana aiki ba dare ba rana, don ceto wasu yara uku da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da su a ranar Laraba, 3 ga Agusta, 2022.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar.
Fanwo ya tabbatar wa mazauna Kogi cewa gwamnati mai ci za ta ci gaba da taka-tsan-tsan wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a inda ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin ci gaba da rike matsayinta na jiha mafi aminci a kasar nan.
Sai dai ya sake nanata dokar hana rufe hanci da gidajen karuwai da gidajen kwana, inda ya jaddada cewa, matakin shi ne na bai wa miyagu mafaka a jihar Kogi.


