Gwamnatin jihar Plateau, ta kwace lasisindukkan makarantun firamare da kuma na sakandari masu zaman kansu a fadin jihar.
Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Elizabeth Wampum, ita ce, ta bayyana hakan a yau Alhamis.
A cewarta, an dauki matakin ne bayan gano cewa, sama da makarantu 5000 na koyarwa ba tare da lasisi ba.
Kwamishiniyar ta ce kashi 90 na makarantu masu zaman kansu a Plateau basa bin ka’idoji da tsare-tsaren gwamnati, inda ta kara da cewa kashi 85 na makarantu 495 masu zaman kansu da aka bai wa lasisi tun da farko basu bi ka’ida ba.
Elizabeth ta ce, ana kuma sanar da al’umma cewa, dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar za su sake sabunta lasisin su.
Gwamnatin ta ce za a yi hakan ne domin gano makarantun da ke koyarwa ba bisa ka’ida ba da kuma taimakawa wadanda doka ta san da zamansu, domin samar da ilimi mai inganci ga kowa.


