Rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta ce, ta kashe wani babban jami’in Hezbollah a harin da ta kai Lebanon ranar Asabar.
Wata sanarwa ta ce Nabil Qaouk, shi ne shugaban sashen tsaro kuma ɗan majalisar ƙungiyar.
Zuwa yanzu Hezbollah ba ta tabbatar da mutuwarsa ba tukunna.
IDF ta ce Qaouk na da kusanci sosai da manyan jagororin Hezbollah, tana mai cewa “da hannunsa a shirya hare-haren ta’addanci kan Isra’ila da ‘yan ƙasarta”. In BBC.