fidelitybank

Mun yi kokari amma an ci mu – Super Eagles

Date:

Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya yaba wa ‘yan wasansa, saboda kwazon da suka nuna duk da rashin nasarar da kungiyar ta yi a hannun Algeria da ci 2-1 a daren Talata.

Najeriya ce ta fara cin kwallo ta hannun Terem Moffi a minti na tara da fara wasa, sai dai Desert Foxes sun yi fafatawa da Riyad Mahrez da Youcef Atal suka zura kwallayen.

Duk da cewa Super Eagles ta yi rashin nasara na uku a wasanni biyar da ta buga a karkashinsa, Peseiro bai damu da sakamakon wasan ba.

“Wasa ne mai kyau, sansanin ya nuna ingancin ‘yan wasanmu da kokarinsu na hadin gwiwa. Wasa ne mai wahala, Algeria kungiya ce mai kyau. ‘Yan wasanmu suna kokarin yin abin da na umarce su da su yi a horo,” Peseiro ya shaida wa NFF TV.

“Yana yiwuwa ku yi rashin nasara a kwallon kafa, ina bakin ciki mun yi rashin nasara. Ba na son yin rashin nasara a wasa, amma ina matukar farin ciki da kwazon ‘yan wasa na. Sun yi kyau a wasan.”

Peseiro, duk da haka, ya yi imanin cewa ƙungiyarsa za ta buƙaci inganta yanayin wasan da za su yi a wasannin gaba.

“Ba mu yi kyau ba wajen kai hari a wasu lokuta, ina ganin za mu iya yin abin da ya fi kyau. Za mu iya inganta wasanmu gaba daya,” in ji tsohon kocin Saudiyya da Venezuela.

“Muna yin kyaun tsaro amma za mu iya kara kai hare-hare da sarrafa kwallon,” in ji shi.

taraba news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp