Ƙasashen Larabawa irinsu Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Qatar da kuma Masar sun mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai wa Iran cikin daren jiya.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce ta yi Alla-wadai da hare-haren Isra’ila kan Iran, inda ta yi kira da “a kai zuciya nesa domin kaucewa yaɗuwar rikici”.
Saudiyya ma ta yi Alla-wadai da harin, inda ta kwatanta shi da matsayin saɓa wa “dokokin ƙasa da ƙasa”, kuma ta buƙaci “dukkan ɓangarori su kai zuciya nesa da kuma rage barazanar yaɗuwar tashin hankali”.
Qatar ta yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai, inda ta kwatanta shi da “saɓa wa” dokokin ƙasa da ƙasa, ta kuma buƙaci “dukkan waɗanda abin ya shafa su guji tayar da hankali”.
Masar ta ce ta damu matuka kan yaɗuwar rikici a Gabas Ta Tsakiya, ciki har da hare-haren Isra’ila kan Iran, inda ta yi Alla-wadai da dukkan matakai da ke kawo barazana ga ɗorewar zaman lafiya a yankin.