Majalisar Dattawa ta amince da dala biliyan 7.8 da kuma yuro miliyan 100 a matsayin kuɗin da Shugaba Bola Tinubu zai ciyo bashi.
Shugaban ya rubuta wa Majalisar wasiƙa yana neman amincewarta game da ciyo bashin a tsarin rance na 2022 zuwa 2024 don kammala wasu ayyuka.
Kazalika, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya sanar da buƙatar Tinubu ta neman amincewa da mutanen da yake son naɗawa a matsayin kwamishinonin hukumar zaɓe ta ƙasa.
Majalisar ta amince da naɗin kwamishinoni bakwai a zaman nata na yau Laraba.