Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya yarda cewa, kulob din ba zai iya siyan ‘yan wasa ba a lokacin kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu saboda ka’idojin wasanni na La Liga.
Laporta, duk da haka, ya dage cewa asusun kulab din yana da “lafiya” kuma, tare da samun kudin shiga a wannan kakar na Yuro biliyan 1.23 da ribar kasafin kudin Yuro miliyan 274.
“Dole ne mu yi wasu levers, wanda ayyuka ne na tattalin arziki da suka ceci kulob din daga lalacewa, kuma a yanzu kulob din yana cikin farfadowar tattalin arziki.
“Amma duk da haka, bisa ga ka’idojin wasan adalci na gasar ta Sipaniya, ba za mu iya sanya hannu ba,” Laporta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Spain EFE.
Ya kara da cewa suna kokarin shawo kan LaLiga “don samun sassauci”.
Barcelona ta sayar da kashi 25% na haƙƙin gidan talabijin na cikin gida da kuma kashi 49% na hannun jari a Studios na Barca akan sama da Yuro miliyan 700.
Wannan ya baiwa Catalan damar fantsama kan Yuro miliyan 150 don kawo Robert Lewandowski, Raphinha da Jules Kounde.
Sun taimaka wa Barca ta zama ta daya a kan teburin gasar Spain da maki 37, biyu fiye da abokan hamayyarta Real Madrid da za su tafi hutun gasar cin kofin duniya na 2022.