Kungiyar farar hula ta Yiaga Africa, dake sa ido kan zaben gwamnan Ekiti, ta yabawa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC bisa kama wasu mutane da ke da hannu wajen sayen kuri’u.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya a kan zaben gwamnan Ekiti na 2022.
Da yake zantawa da manema labarai a Ado Ekiti, Babban Darakta na Yiaga Africa, Samson Itodo, ya kira jami’an EFCC da aka tura domin tabbatar da gurfanar da mutanen da aka kama da laifin satar kuri’u.
Yiaga Africa ya lura cewa an hana masu kada kuri’a kada kuri’a duk da cewa sun rike katin zabe na INEC a wuraren da kungiyar ta lura.