Babban hafsan hafsoshin kasa, Manjo Janar Christopher Musa da babban hafsan sojin ƙasa Manjo Janar Toareed Lagbaja, sun yaba wa dakarun sojin ƙasar musamman waɗanda ke fagen daga, bisa sadaukarwa da kishin ƙasa da jajircewa da suke nunawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da haɗin kan ƙasar.
“Tabbatar da tsaro da ci gaban ƙasarmu wani babban nauyi ne da ya rataya a wuyan kowanne ɗan Najeriya”, kamar yadda dakartan yaɗa labaran hukumar tsaron ƙasar ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin babban hafsan tsaron ƙasar.
Janar Musa ya tabbatar wa jami’an tsaron ƙasar irin goyon bayan da yake ba su a ƙoƙarinsu na gudanar da ayyukansu.
A nasa ɓangare, babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar Manjo Janar Toareed Lagbaja ya yaba wa sojojin ƙasa na Najeriyar dangane da saudaukarwa da jajircewa da ya ce sojojin na nunawa wajen gudanar da ayyukansu a faɗin kasar.
Ya kuma yi kira ga dakarun sojin su ci gaba da nuna jarunta da kishin ƙasa a yayin gudanar da ayyukansu.
A makonni biyu da suka gabata ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar, bayan sauke tsoffin dakarun tsaron.