Kungiyar dalibai musulmi ta kasa reshen jihar Legas (MSSN) ta yaba da hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya dace da amfani da hijabi a makarantun mallakar gwamnati a jihar.
A hukuncin da kotun kolin ta yanke a ranar Juma’a, ta tabbatar da hakkin dalibai mata musulmi na saka hijabi a makarantun firamare da sakandare na gwamnati a Legas.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, shugaban kungiyar MSSN a jihar Legas, Miftahudeen Thanni, ya bayyana farin cikinsa da cewa dalibai mata musulmi yanzu za su iya sanya hijabi zuwa makaranta ba tare da tsangwama ba.
A wata sanarwa da ta fitar jim kadan bayan kotun kolin ta yanke hukuncin, Thanni ya ce hukuncin ya karawa daliban kwarin gwiwa a bangaren shari’a.
Ya ce, “Hukuncin kawai yana nufin cewa duk da cewa hijabi ba ya wajaba a makarantun Legas, amma daliban musulmin da ke son sanya shi suna da ‘yancin yin hakan kuma a bisa doka.
“Mu kungiya ce mai bin doka kuma za mu ci gaba da bin dokar kasa. Mun yaba da hukuncin. Matsayin doka ya fito fili a kan batun. Wannan al’amari ya sake tabbatar mana da cewa duk bege bai rasa nasaba da samun al’umma ta gari.
“Kada gwamnati ta yi yaki da matasan da suka zabi suturce tsiraicinsu tare da karfafa masu tafiya tsirara da aikata haramun a bainar jama’a.”