fidelitybank

Mun tantance Daliban da za su karatu waje su 1,1010 – Gwamnatin Kano

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta kammala shirin fara daukar nauyin daliban manyan makarantu 1,010 a gida da waje a kashi na farko na tallafin karatun da za ta yi.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr. Yusif Ibrahim Kofar Mata, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin kwamishinan yada labarai.

 

Da yake jawabi ga manema labarai, Kwamishinan ya bayyana cewa an kafa kwamitin tantancewa na sake dawo da shirin daukar nauyin daliban da suka kammala karatu a Kano domin samun digiri na biyu a jami’o’in cikin gida da na ketare, an kafa tare da kaddamar da kwamitin a ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Ya kara da cewa, kwamitin ya karbi takardun neman shiga cikin shirin daga mutane sama da 1200, Kuma ya zuwa yanzu an tantance sama da mutane 800, kuma har yanzu ana cigaba da tantancewar kuma za a fitar da cikakkun bayanai na wadanda suka sami nasara nan ba da jimawa ba.

“Yana da matukar muhimmanci a sanar da al’ummar Kano cewa, dawo da wannan shiri da gwamnatin Abba Kabir Yusif ta yi, ba wai kawai don samawa ‘yan jihar Kanon takardar shaidar kammala digiri ba, a’a, a’a, a’a, shirin zai karawa matasanmu kwarin gwiwa da kuma kara samun damammaki a fannoni daban-daban waɗanda wataƙila za su iya taimakawa wajen sauya matsayin jiharmu a idanu duniya”.

Kwamishinan wanda kuma shi ne sakataren kwamitin maido da manufofin Kano na bayar da tallafin karatu ya bayyana cewa maido da manufar bayar da tallafin karatu ga ‘yan asalin jihar Kano don yin manyan digiri a ciki da wajen kasar nan an yi shi ne da niyyar bunkasa rayuwar al’ummar Kano da Nigeria baki daya. In ji Kadaura.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp