A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa suka tabbatar da amincewa da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda jigo ne a haɗakar ya ce: “mun kwashe wata tara zuwa shekara ɗaya muna tattaunawa domin ganin yadda za mu haɗa kanmu mu shiga jam’iyya ɗaya da ba za a iya soke rajistarta ba, mu gyara jam’iyyar da shugabancinta da aƙidarta da fito da tsarin da zai ceci ƙasarmu daga wannan hali da aka shiga.”
Hakan na zuwa ne bayan yunƙuri daban-daban da ƴan adawar suka yi na ganin sun samar da ƙwaƙƙwarar adawa da za su iya tunkarar shugaban ƙasar mai ci Bola Ahmed Tinubu, wanda suke zargi da gazawa a mulkinsa.