A karon farko, Koriya ta Arewa ta amince da barkewarta cutar korona a hukumance.
Kafofin yada labaran kasar sun ce Shugaba Kim Jong-un ya jagoranci wani taro don tattauna abin da ya bayyana a matsayin “babban abu da ke bukatar a ba shi kulawar gaggawa.
Barkewar wadda aka fara ganowa a babban birnin kasar Pyongyang ranar Lahadi, ta hada da nau’in Omicron mai saurin yaduwa.
Wakiliyar BBC ta ce, mai yiwuwa ne an samu wadanda suka kamu a baya, da mahukunta suka yi tunanin za su shawo kan lamarin cikin hanzari.
Ba a bayar da cikakken bayani kan adadin wadanda suka kamu da cutar ba.
Koriya ta Arewa ta rufe iyakokinta a farkon barkewar cutar kuma ta yi ikirarin hana ta shiga kasar a wancan lokaci.