Ofishin Hukumar kare haƙƙin bil’adama ta kasa a jihar Kano, ya ce, ya samu rahoton cin zarafi mai nasaba da jinsi guda 1,300 daga watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2022.
Kuma a cewar shugaban ofishin, Shehu Abdullahi, ƙananan yara ƴan ƙasa da shekara tara ne suka fi fuskantar cin zarafin, haka nan lamarin ya kai ga mutuwar wasu daga cikin su da kuma haifar da lalurar ƙwaƙwalwa.
Abdullahi ya bayyana haka ne a wani taron da aka gudanar domin tunawa da ranar masu fafutika ta duniya, ta shekarar 2022.
Jami’in ya ce ya zama wajibi a haɗa hannu tsakanin masu ruwa da tsaki domin kawar da matsalar.