Dakarun Operation Hadin Kai a makwanni biyu da suka gabata sun yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda akalla 47 tare da kubutar da Mary Dauda daya daga cikin ‘yan matan da aka sace a shekarar 2014 a garin Chibok da ke Borno.
Manjo Janar Bernard Onyeuko, Darakta mai kula da harkokin yada labarai na tsaro ne ya bayyana haka a taron shalkwatar tsaro na mako biyu a ranar Alhamis a Abuja.
Onyeuko ya ce, a ranar 12 ga watan Yuni ne sojojin suka yi arangama da ‘yan ta’addan a lokacin da suke aikin share matsugunin su a Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.
Ya ce, sansanin da ake kira Markas ko Hedikwatar ‘yan ta’addan ya yi garkuwa da dimbin ‘yan ta’adda da iyalansu.
A cewarsa, an kashe ‘yan ta’adda kusan 47 ciki har da manyan kwamandojin su bayan wani kazamin fada da aka gwabza.
A kokarin ceto ‘yar Chibok, Onyeuko ya ce sojojin na 26 Task Force Brigade da ke aikin share fage a Ngoshe sun tare Miss Mary Dauda mai shekaru 27 da yaronta.
Ya ce, wanda aka kashen, wanda ke cikin jerin sunayen ‘yan matan Chibok na 2014 mai lamba 46, ana zargin ya tsere ne daga Gara da ke karamar hukumar Gwoza ta Borno.