Gwamnatin Tarayya ta ce, ta samu duka kuɗin gudanar da aikin gina layin dogo daga birnin Maiduguri na jihar Borno zuwa garin Aba na jihar Abiya.
Ministan Sufuri Saidu Alkali ne ya bayana hakan a yau yayin wani taron bita da ake gudanarwa a Kaduna, kamar yadda wata sanarwa daga ofishinsa ta bayyana.
“Layin dogon mai tsawon kilomita 1,443 zai ratsa jihohin Borno, da Yobe, da Gombe, da Bauchi, da Filato, da Kaduna, da Nasarawa, da Binuwai,” in ji sanarwar da kakakin ministan Rabiu Ibrahim ya fitar.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana inda gwamnatin ta samo kudin ba. Akasarin manyan ayyuka masu tsada kamar wannan akan yi su ne ta hanyar bashi ko kuma lamuni.
Ministan ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gyara layin dogo na dakon kaya tsakanin Legas zuwa Kano.