fidelitybank

Mun samu gagarumar nasara a hukumar mu – EFCC

Date:

Hukumar EFCC ta ce a shekarar 2024 ta samu nasarar da ba ta taɓa samu ba tun da lokacin da aka ƙirƙire ta.

Ta ce a shekarar ta ƙwato kuɗaɗe da suka haɗa da naira biliyan 364.6 da da dala miliyan 214.5 da fan 54,318.64 da yuro 31,265 da kuɗin ƙasar Canda, dala 2,990 sai kuma kuɗin ƙasar Australia, dala 740, kamar yadda ta bayyana.

Wasu kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato sun haɗa da CFA7,821,375 da dirham ɗin UAE 170 da riyal 5,115 da W73,000, yen 105, da GH¢ 225 da rand 50.

Hukumar ta ƙara da cewa a shekarar ce ta ƙwato rukunin gidaje 750, wanda shi ne mafi girma a tarihin hukumar.

Haka kuma ta ƙwato kuɗaɗen kirifto irin su Bitcoin guda 13.37 wanda darajarsu ta kai dala 572,992.86 da Ethereum 5.97886094 masu ƙimar dala 13,353.06 da USDT 1,002.547631 da sauransu.

Hukumar ta kuma ƙwato kamfani da otel da zinare da fulotai.

Hukumar ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe guda 15,725, ta gurfanar da mutane aƙalla 5,083 a kotu, ta samu nasara a shari’a guda 4,011.

Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa ta samu wannan nasarar ce ta hanyar aiki da jajircewar jami’anta wajen yaƙi da almundahana da sauran laifuka a ƙasar baki ɗaya.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp