Rundunar soji ta ce, dakarunta sun samu gagarumin nasara a wani farmaki da suka kai ranar Alhamis kan sansanonin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram a jihar Borno.
Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ya ce dakarun na Operation Hadin Kai sun kai harin ne a wani yanki da ke kan hanyar Wajiroko zuwa Damboa, wanda ya zarce zuwa Maiduguri.
A lokacin harin, sanarwar ta ce an hallaka mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP da dama.
Haka nan dakarun sun ƙwato bindigogi da harsasai, da motoci da kuma kayan yaƙi da dama.