fidelitybank

Mun sami harajin tiriliyan 5.5 – Hukumar Haraji

Date:

Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta ƙasa (FIRS), ta bayyana karɓar harajin naira tiriliyan 5.5 tsakanin watan Janairu zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Shugaban hukumar Muhammad Nami ne ya bayyana haka a lokacin taron Majalisar tattalin arzikin ta ƙasar da ya gudana ranar Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar de ke Abuja.

Wannan ne karo na farko da hukumar ta tara adadi mafi yawa na kuɗin haraji a cikin wata shida, kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar.

Rahoton da Muhammad Nami ya gabatar wa majalisar tattalin arzikin, ya nuna cewa abin da hukumar ta tara ya zarta abinda ta ƙiyasta samu a cikin rabin shekarar.

Tun da farko hukumar ta ƙiyasta tara naira tiriliyan 5.3 a cikin wata shidan farko na shekarar.

Rahoton ya kuma nuna cewa kuɗin harajin da hukumar ta tara a ɓangaren man fetur, naira tiriliyan 2.03 ne ya fi yawa cikin harajin da hukumar ta tara.

Sai kuma naira tiriliyan 3.76 da hukumar ta tara daga sauran bangarorin.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp