Gwamnatin tarayya ta ce, ta samar da ayyukan yi ga matasa har 750,000, domin cike giɓin da ake da shi na rashin ayyukan yi a kasar.
Babban daraktan hukumar da ke lura da sake fasalin aikin gwamnati, Dasuki Arabi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na NAN, a ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce,”An samu nasarar hakan ne, bayan wani bincike da muka yi na NESC kan rashin aikin yi a Najeriya shi ne muka zo da wasu tsare-tsare masu kyau.
“Taron ya zo da wasu hanyoyin samar da ayyuka 750,000 da kuma tuni gwamnati ta aiwatar da su kan matasa da matsalar rashin aikin yi,” in ji Arabi.
Ya kuma ce, suna aiki tare da babban bankin kasar da SMEDAN domin taimaka wa ɗinbin marasa aikin yi a kasar.