Hukumomin harkokin lafiya, sun rufe akalla gidajen sayar da magunguna 25,000 waɗan da ba bisa ka’ida ba a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Magatakardar hukumar kula da harhada magunguna ta kasa (PCN) mai barin gado, Iliya Mohammed ne ya bayyana hakan a wajen taron baje kolin katin zabe na jama’a a Abuja ranar Talata.
Mohammed ya ce, an rufe wuraren ba bisa ka’ida ba ne, saboda wasu dalilai da suka hada da rashin tsafta, rashin cikakkun takardu, da kuma daidaita takardu. In ji Premium Times.
“Gidan magunguna ba bisa ka’ida ba da aka rufe a cikin shekaru takwas da suka gabata sun haura 25,000 a fadin kasar nan.