Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce, gwamnatinsa ta rage yawan ‘yan fashi da makami zuwa kashi 70 cikin 100 a cikin shekara daya.
A cewar Radda, hakan ya biyo bayan yadda aka samu hadin kai tsakanin jami’an tsaron gida da na jami’an tsaro na yau da kullum a fadin jihar.
Radda, wanda ya kai ziyarar aiki a Yola, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ranar Asabar.
Ya ce, “Lokaci ya yi da za a saka ‘yan sandan jihohi a cikin yaki da rashin tsaro a kasar nan.
“Mun rage yawan ‘yan fashin zuwa kusan kashi 60 zuwa 70 cikin 100. Abin da muke gani a yanzu shi ne irin hauka da ‘yan fashin ke bi na zuwa kauyukan da ke da wuyar isa ga dazuzzuka, suna kona gidaje da kashe mutane.
“Mun kirkiro dabarun yakar ta.”
Radda ya ci gaba da bayanin cewa galibin kasashe masu tasowa suna da ‘yan sandan jihohi da ke tsaron rayuka da dukiyoyi.
Ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su baiwa ilimi fifiko domin ci gaban kasa.
Radda ya ce, “Wannan zai ba da dama ga masu karamin karfi, don samun ilimi mai inganci a kowane mataki.”